Wani Neman Jarumai . Морган Райс
Чтение книги онлайн.

Читать онлайн книгу Wani Neman Jarumai - Морган Райс страница 9

СКАЧАТЬ duniyan na kewayawa ayayinda yake tunanin wani irin karfi ne yashigeshi, abinda wannan yake nufi, asalin mutumim dashi ya kasance. Mutanen da aka sansu da irin wannan karfin su Druid ne kawai. Amma kuma ai mahaifinsa da mahaifiyarsa basu kasance Druid ba, saboda haka bazai yiwu shi ya zama daya ba.

      Ko kuma zai iya zama ne?

      Dayaji Kaman da mutum a bayansa, Thor ya juyo yaga Argon a tsaye a wurin, yana kallon dabban a kasa.

      “Da yaya kazonan?” Thor ya tambaya, yana mamaki.

      Argon yayi Kaman bai jishiba.

      “Ka shaidi abinda ya faru?” Thor ya tambaya, har yanzu bai yarda ba. “Ban san yanda na aikatashi ba.”

      “Amma kasani,” Argon ya ansa.”A can ciki, kasani. Kai daban ne da duka shauran.”

      “Yayi kama da…..muhimmin Karin karfi,” Thor yace. “Kaman karfinda nima bansan inadashiba.

      “Kewayen makamashin,” inji Argon. “Watarana zakazo kasanshi da kyau. Zaka ma iya koyan gudanar dashi.”

      Thor ya kama kafadarsa; zafin yayi tsanani. Ya kalli kasa ya hangi hanunsa a rufe da jinni. Yaji kansa ba nauyi, yana damuwan abunda zai iya faruwa idan bai samu taimako ba.

      Argon yayi taku uku zuwa gaba, ya mika hanu, ya riko hanun Thor da baya komai, ya daura shi da kyau a kan mikin. Ya rikeshi a wurin, ya mayar da kansa baya, sai ya rufe idannunsa.

      Thor yaji wani yanayi mai dumi a cikin hannun nasa. Cikin dakikoki, jinin dake kan hannunsa ya bushe, kuma yaji zafin dayakeji ya fara raguwa.

      Ya kalli hannun ya gagara ganewa: ya warke. Abinda ya rage a wurin kawai shine tabon idanun inda farcen dabban ya yankeshi – amma suma a toshe suke kuma sun yi Kaman sun kwana biyu. Jinin ma ya saya ya daina zuba.

      Ya kalli Argon da mamaki.

      “Yaya kayi wannan?” ya tambaya.

      Argon yayi murmushi.

      “Baninayiba. Kaikayi. Nina baiwa karfinka ummurni ne kawai.”

      “Amma bani da karfin warkaswa,” Thor ya ansa, yana mamaki.

      “Bakadashi?” Argon ya ansa masa.

      “Bangane ba. Babu wani abu da yayi daidai da tunani a nan,” Thor yace, rashin hakurinsa na karuwa. “Yi hakuri, gaya mani.”

      Argon yaki ya kalleshi.

      “Wassu abubuwa a cikin lokaci zakazo kasani.”

      Thor yayi tunanin wani abu.

      “Yanzu wannan na nufin zan iya shiga rundunan sarki kenan?” ya tambaya, da faraha. “Tabbattace, idon zan iya kasha dabban Sybold, to zan iya kare kaina a wurin shauran yaran.”

      “Tabbatace zaka iya,” ya ansa masa.

      “Amma sun zabi yan’uwana – basu zabeniba.”

      “Yan’uwanka bazasu iya kashe wannan mummunan dabban ba.”

      Thor nata maida kallo, yana tunani.

      “Amma ai sun riga sun kini. Dayaya zan shiga?”

      “Daga yaushe jarumi ya fara bukatan a gaiyaceshi?” Argon ya tambaya.

      “Kalmominsa sun shiga da zurfi. Thor yaji jikinsa gabadaya ya fara dumi.

      “Kana nufin inje a ganni kawai kenan? Ba tareda an gaiyace ni ba?”

      Argon yayi murmushi.

      “Kai kana iya halittan kaddararka. Wasu basu iyawa.”

      Thor ya kifta ido – kuma jimkadan, Argon ya bace. Kuma.

      Thor ya juya, yana kallon kota ina, amma babu wani alamansa.

      “A tanan!” inji wani murya.

      Thor yajuya sai yaga wata katuwar dutse a gabansa. Yaji Kaman muryan yazo daga saman dutsen, sai yayi hanzari ya haura babban dutsen.

      Ya kai saman, amma ya kidime da baiga ko alaman Argon ba.

      Daga wannan wuri mai kyau, amma, ya iya gani samada itatuwan dajin Darkwood. Ya hangi inda Darkwood takare, yaga wata rana tana sauka a cikin launin ganye mai zurfi, kuma a gabada wannan kadan, hanyar zuwa fadan sarki.

      “Kana iya bin hanyan,” muryan ya dawo. “Idan kanada zuciya.

      Thor ya juyo amma baiga komai ba. Kaman murya ne kawai, yana dawowa. Amma yasan Argon na nan, a waniwuri, yana zigashi. Kuma yaji, daga zurfin zuciyarsa, cewa yanada gaskiya.

      Batare da wani kwokwanto ba kuma, Thor ya sauko daga saman dutsen sai ya pasa cikin dajin ya nufi hanya mai nisan.

      Yana gudu a hankali zuwaga kaddararsa.

      SURA NA UKU

      Sarki MacGil – kakkaura, mai fadin kirji, dagemu mai fararen gashi da yawa, dogon tsuma daidai da gemun da kuma goshi mai fadi da ya jera yaki da yawa – na saye a saman makiriyar fadansa, sarauniyarsa a gefensa, suna kallon abubuwan wakanan ranan na bukukunan shekara. Daular sarautarsa na shimfide a kasa a cikin duk matsayinsu, amike har zuwa iya ganin ido, birni mai tasowa a kewaye da katangun duwatsu irin na daa. Fadan sarki. Aharhade ta cunkusun angwayoyi masu gidajen duwatsu kowane iri – gidajen jarumai, masu bada kula, dawakai, yan Silver, rundunan sarki, masu gadi, barikin mayaka, dakin makamai, ma’ajiyin manyan makamai – kuma a sakanin duk wannan, darurukan wuraren zama wa dimbim mutanensa da suka zabi zama a cikin katangun birnin. A sakanin wadannan angwani akwai ciyayi, lambun gidan sarauta, wuraren kasuwanci a jere da duwatsu, mabulbulan ruwa. Fadan sarki yayita samun kwaskwarima tun shekaru aru aru, daga mahaifinsa, daga mahaifin mahaifinsa kafin shi – kuma yanzu birnin na kololuwar haskakawanta. Babu wani tantama, birnin ta kasance mafi kwaciyan hankali a dukkan yammacin daulolin zoben a yanzu.

      MacGil yasamu baiwan mafi kyawun da mafi biyayya na jarumai da a ka taba gani, kuma a rayuwarsa, bawanda ya isa ya kawo hari. Ya kasance MacGil na bakwai da ya riki sarautan, yakuma rike da kyau a cikin shekaru talatin da uku da yayi yana mulki, yakasance sarki mai adalci da kuma wayo. Kasar ta samu cigaba mai girma a zamaninsa. Ya ninka adadin mayakansa, kara girman biranai, kawo ma mutanensa cigaban arziki, kuma babu kokaawa koda guda daya da aka samu daga talakawansa. Ansanshi a matsayin sarki mai sake hanu, kuma ba a taba samun zamanin dayazo da cigaban arziki da zaman lafiya Kaman wannanba tunda ya hau mulkin.

      Wanda, basafaiba, yakasance ainihin dalilin dayasa MacGil baiyi baci a darenanba. Saboda MacGil yasan tarihin kansa: a duk shekarunnan, ba a taba samun rata mai tsayi Kaman haka babu yakiba. Ya daina kwokwanton ko za a kawo hari ko baza a kawoba – abinda ya rage yasani kawai dayaushe. Kuma daga wane.

      Barazana mafi girma, ai dama, daga wajen zoben yake, daga daulolin marasa hankali da suke mulkin yanhayaniyan da suke tawaje, da suke mulkin dole a kan mutanen wajen zoben, gaba da koraman. Wa MacGil, da nasaba bakwai da suka rigayeshi, kasashen wajen basu taba kasancewa wani barazanaba. Saboda inda daularsa ta samu kanta a doron kasa, a kewaye daidai kota ina – Kaman zobe – arabe kuma daga shauran duniya da loto mai zurfi da kuma fadin mil daya, kuma wanda take da kariyar wata СКАЧАТЬ