Название: Wani Neman Jarumai
Автор: Морган Райс
Издательство: Lukeman Literary Management Ltd
Жанр: Героическая фантастика
Серия: A Jeren Zoben Mai Sihiri
isbn: 9781632912473
isbn:
Anyi wa wannan littafin lasisin amfani dashi domin jin dadin kanka ne kawai. Ba a yadda ka sayar dashi ko ka badashi kyauta ba. Idon zaka so ka raba shi da wani, yi hakuri ka sayi wani wa kowane mai karantawa. Idon kana karatun wannan littafin ba tare da ka saya bane, kokuma ba a saya domin amfaninka bane, yi hakuri ka mayar sai ka sayi naka. Nagode maka saboda baiwa aikin da wannan mawallafin yayi tukuru muhimmanci.
Wannan labari ne irin na tasuniya. Sunaye, yanayi, sanao’i, kungiyoyi, wurare, abubuwan dasuka auku dukansu sun kasance tunanin marubuci ko labarin tasuniya. Kama da wani mutum araye ko mace da zasuyi sosayine.
Hoton bayan marfin littafi kareriyar aikin fasaha na razoom game, anyi anfani dashi a karkashin lasisin Shutterstock.com.
ABIN DA KE CIKI
“kan da yasa hulan sarauta baya samun sauki”
--William Shakespeare
A Littafin Henry IV, Shashi na biyu
SURA NA DAYA
Yaron ya tsaya a kan kololuwar karamar tudun kasar da take kasa kasa a masarautar yamma na zoben, ya kalli arewa, yana kallon farkon tasowan rana. A iya nisan kallonsa, yana ganin koren shinfidaddun tudu, wayanda suna sauka su haura kaman tozon rakumi a cikin wadansu kwari da ganiyan tudu. Hasken bullowan ranar farko mai launin ruwan lemu ya dan dade yana haskawa a kan rabar safe, yana sa su kyalli, yana ara wa hasken, majigin da yayi dede da yadda yaron yake ji a ran sa. Yaron bai cika tashi da wuri haka ba kuma bai taba nisan kiwo daga gida haka ba – kuma bai taba haurawa tudun da tsawo haka ba – domin yasan yin hakan zai jawo fushin mahaifinsa. Amma a wanan ranar, bai damu ba. A wannan ranar, yayi biris da miliyoyin dokoki da ayyuka masu yi masa danniya na tsohon shekaru goma sha hudu. Hakan ya faru ne saboda wannan ranan na daban ne. Rana ne da ya kasance kaddararsa ta iso.
Yaron, Thorgrin na masarautar yammacin daular yan dangin McLeod na kudu – sananne ga duk wadanda yaso da suna Thor kawai – dan auta cikin yara maza hudu, mafi karacin soyuwa a wurin mahaifinsa, ya kwana idonsa biyu saboda begen wannan rana. Yayi ta juye-juye, da idanu cike da ruwa, yana jira, yana fatan farkon tasowan rana. Saboda rana kamar haka yakan faru ne sau daya a cikin shekaru da yawa, kuma in har ya bar zarafin ya kubuce masa, zai makale a wannan kauyen, yakuma dawwama a aikin kula da garkunan mahaifinsa har iya rayuwarsa. Wannan kuma ya zama tunanin da ba zai iya hakuri da shi ba.
Ranar shiga soja . Ya kasance rana daya ne rak da sojojin sarki ke zaga wa duka dauloli suna zaban masu son shiga rundunan sarki. Tun da yake raye, Thor baya mafarkin komai face wannan. A wurin shi, ma’ anar rayuwa abu daya ne rak: shiga silver, zababbun hafsosin rundunar sarki, sanye da kayan adon yaki mafi kyau da kuma tattatun makamai a ko ina a cikin duka masarautai biyun. Kuma ba a shiga cikin silver sai mutum ya shiga babbar runduna, rundunonin masu koyan aikin tsaro da shekarun su ke sakanin goma sha hudu da goma sha tara. Kuma idon mutum bai kasance dan fittatun mutane ba, ko wani sanannen jarumi ba, to babu wata hanyar shiga babbar runduna.
Ranar shiga soja ne kawai ta sha banban, wannan abin ba safai ba, da ya ke faruwa a kowani shekara da rundunonin sarki ke raguwa kuma hafsosin sarki ke zaga kasan suna neman sabbobin dauka. Kowa ya san kalilan a ke daukawa a cikin yaku bayi – kuma musamman an san kadan ne daga ciki za su samu shiga babban runduna.
Thor ya karanci yanayin wuri sosai, yana dubawa ko zai ga wata alamar motsi. Yan silver, ya sani, ya zama dole su biyo nan, hanya makadaiciya zuwa kauyen sa, kuma yaso ya zama wanda zai fara ganin su. Garken tumakin sa na ta nuna rashin yarda a kewaye da shi, sun tada kukan haushi da murya daya kuma suna nuna su fa ya mayar dasu gangarar tudu, inda mafi kyawun ciyayi suke. Yayi kokarin ya toshe ihunsu, da kuma warinsu. Sai ya zama masa dole СКАЧАТЬ